• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Dole Kowacce Ma’aikata Ta Tabbatar Da Tsaftar Bandakunan Ta — Gwamnatin Kano

BySani Magaji Garko

Sep 27, 2024

Gwamnatin jihar Kano ta ce dole ne kowacce ma’aikata ko hukuma ta tabbatar da tsaftar muhallin ta musamman bandakuna domin Inganta lafiyar alumma.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Alhaji Nasiru Sule Garo ne ya bayyana hakan bayan kammala tsaftar muhalli ta kasuwanni, ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ake gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a Kano dake Arewacin Nigeriya.

Ya ce a ziyarar da ma’aikatar take kaiwa ma’aikatun da hukumomin gwamnati, babbar matsalar da ake gani itace kazanta ko kuma lalacewar bandakuna.

KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Zamu Girmama Shawarwarin Yan Kasuwar Kano — Shugaban REMASAB

“Ma’aikatar ayyuka da muka ziyarta, tsakar gidan tana cikin tsafta, amma suna tara shara ta dade ba’a kwashe ba, shi yasa muka basu shawara lallai su yi aiki da hukumar REMASAB domin a rika kwasheta akan lokaci. A ma’aikatar ayyuka kuma kamar yadda aka saba gani a sauran gurare suma bandakunan su ba shi da kyau, amma mun umarce su lallai su gyara gami da tabbatar da suna cikin yanayi Mai kyau wanda kowa zai iya amfani da su,” inji Garo.

“Suma hukumar KANGIS wacce yanzu muke a ciki gashi mungani suna aikin gyare-gyare, kuma mun shawarce su lallai su tabbatar an samar da ingantattun bandakuna wanda kananan ma’aikata da masu ziyartar Ofishin zasu rika amfani da shi,” inji Kwamishinan.

Nasiru Garo ya kuma ja kunnen matukar baburan Adaidaita sahu da su guji karya dokar tsaftar muhalli domin an tanadi kotun tafi-da-gidanka don hukunta duk wanda ya karya doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *