• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Za Mu Tabbatar Da Kwashe Dukkan Sharar Kofar Wambai — Getso

ByGlobal Tracker

Feb 24, 2023

Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano ta ce zata tabbatar da an Kwashe Dukkan Sharar da aka tara a Yankin Malafa da ke Unguwar Kofar Wambai cikin Karamar hukumar Birnin Kano da kewaye.

Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a lokacin tsaftar Muhalli ta Juma’a da Asabar din karshen wata wacce aka hade tare da gudanar da ita saboda zaben shugaban kasa da Yan majlisu da za’ayi a gobe Asabar.

Getso wanda mai rikon mukamin babban sakataren ma’aikatar Dakta Garba Sale ya wakilta ya ce sharar da take badalawa Kofar Wambai ta Dade ana tara ta kuma dama akwai wajen zuba shara da Gwamnati ta samar domin tarawa tare da debe ta domin kaita guraren da ake zubarwa.

KU KARANTA: Mutanen Kano Na Murnar Kwashe Sharar Da Gwamnatin Kano Ta Yi

Ya ce dukkanin manyan motocin diban shara za’a girke su ne a Unguwar ta Kofar Wambai domin tabbatar da an debe sharar.
Kwamishinan ya kuma yabawa yadda mahukuntar kasuwar Kofar Singa suka tsaftace ta yana mai cewa a wannin baya da aka je har tarar shugabannin kasuwar aka ci, amma a wannan lokacin sun gyara kura-kuran da suka yi a baya.

Daga nan ya yabawa al’ummar Kano bisa yadda suka zauna a gidajen su tare da aiwatar da tsaftar Muhalli kamar yadda ya da ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *