• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Maulidi: Nutsuwa Wajibi Ce Ga Musulmi a Lokacin Ambaton Manzon Allah — Ibrahim Khalil

BySani Magaji Garko

Oct 13, 2024

An bayyana amana da nutsuwa a matsayin wasu daga cikin manyan abubuwan da suke tabbatar da ingancin taron Maulidi a fadin Duniya.

Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khaleel ne ya bayyana hakan a daren jiya yayin wani taron Mauludin fiyayyen Halitta Manzo ( S.A.W ) da aka gudanar a garin Kano.

A cewarsa, Nutsuwa wata sifface da ta kamata a ce duk wani musulmi a duniya ya suturta kanshi da ita musamman a guraren da ake ambaton ALLAH da manzonsa, kamar taron Maulidi da masallatai da sauran guraren da ake daukaka kalmar Allah.

KU KARANTA: 

Ya ce, dole ne duk wata halittar data kasance a tarukan Maulidi musamman ma mutane dasu zama masu nutsuwa da tattara hankali guri guda domin jin yadda halitta da halayen Manzo ( S.A.W ) suke.

Koda yake zantawa da Manema Labarai a gefen taron Maulidin, Sheikh Khaleel ya ce wajibine mutane su zama masu nutsuwa a lokacin da ake zancen Addinin Musulunci.

A taron Maulidin manyan malaman Addinin Musulunci a Nigeria dama irinsu Mal. Nasidi Abubakar G/Dutse da Malam Ibrahim Me-ashafa da kuma Farfesa Umar Sani Fagge, da sauran Malamai ne suka gabatar da mukaloli akan fiyayyen hakitta Annabi Muhammad (S.A.W).

“Halartar taruka irin haka dai na kara sanya nutsuwa da Il-hama a zukatan wadanda suka halarta,” inji Naseer Sa’id Adahama, daya daga cikin malaman ya fada.

Taron maulidin wanda shi ne karo na 17 da fara gudanarwa da kuma aka gudanar a Unguwar Nassara G.R.A dake Kano, ya kunshi manya da kananan malaman Addini musulunci da ‘yan kasuwa da Yan siyasa da sauran al’umma inda aka yi Addu’o’in samun zaman lafiya ga jihar Kano, arewa dama Nigeriya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *