• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Kayar Da Duk Dan Majalisar Da Ya Goyi Bayan Sauya Fasalin Harajin Tinubu — Falakin Shinkafi

BySani Magaji Garko

Nov 28, 2024

Al’ummar arewacin Nigeriya na cigaba da Allah wadai da tsarin sauya fasalin harajin da shugaban Nigeriya Bola Ahmed Tinubu ya ke kokarin yi lamarin da ya sa ya rubutawa majalisar dattawan Nigeria wasika gami da kunshin sabon tsarin dokar da yake so majalisar ta yi aiki akan domin amincewa.

Daya daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a Nigeriya Falakin Shinkafi Ambasada Yunusa Yusuf Hamza a wani sakon murya da aka nada ya kuma aikowa GLOBAL TRACKER, basaraken ya ce abin takaici ne ace wani dan majalisar dattawan ko wakilai daga arewacin Nigeriya ya goyi bayan kudirin shugaban kasa na sauya fasalin haraji wanda ba shi da wata manufa da ta wuce karo talauci da koma bayan tattalin arzikin Arewacin Nigeriya tare da Inganta cigaban jihar Legas.

Basaraken ya ja kunnen yan siyasa musamman yan majalisar dattawan da takwarorinsu na wakilin cewa “duk wanda ya goyi bayan kudirin shugaban kasa na sauya fasalin harajin to yan arewa zasu tabbatar bai koma kujerarsa ba a shekarar 2027 idan zaɓe ya zo.”

KU KARANTA: Zamu Bijiro da Hanyoyin Bunkasa Safarar Dabbobi a Nigeria — Mustapha Ali

Yanzu haka dai an yiwa kudirin dokar karatu na biyu a majalisar dattawan Nigeria wanda sanatan Kano ta arewa kuma matemakin shugaban majalisar dattawan Barau Jibril ya jagoranta.

An dai shiga rudu a Majalisar a jiya Laraba bayan da akayi cushen kudirin dokar, wacce nan take sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya ja hankalin Barau cewa kuskure ayi cushen kudirin dokar bayan al’ummar arewacin Nigeriya sun nuna kin amincewa da tsarin.

“Mu yan arewa bamu yadda da wannan doka da akayi wa karatu na biyu a majalisar ba, saboda haka muna kira da kakkausar murya ga sanatocinmu na arewa gaba daya cewa kada muji, kada su yadda wannan doka ta wuce, idan kuma suka yadda ta wuce zasu gamu da fushin mu, babu yadda za’ayi a rusa jihohin mu gaba daya na arewa a je a Inganta wata jiha kwaya daya (Legas),” inji shi.

“Idan aka yi wannan doka, masifar da za’a shiga a Nigeriya sai tafi ta cire tallafin man fetir, duk kuma wanda ya bada goyon baya, to ya kuka da kansa, domin zamu tabbatar an kayar da shi a zaɓe,” inji Falaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *