• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Fito Da Sabbin Manufofin Kara Daga Darajar Karatun Alkur’ani — Shugaban Jami’ar KHAIRUN

BySani Magaji Garko

Dec 5, 2024

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu KHAIRUN ta sha alwashin kara daukaka daraja da matsayi na ilimin alkurani mai girma ta hanyar koyarwa da bincike da kuma rubuce-rubuce a fannoni daban-daban na Alkur’ani mai girma.

Shugaban jami’ar Farfesa Abdurrashid Garba ne ya bayyana hakan a yayin da cibiyar kasa da kasa don Nazari kan kimiyyar Alkurani wato “International Institute of Qur’anic Science” ta shiryawa mahaddata alkurani bita ta yini daya wadanda aka zabo mutane biyu daga kowacce karamar hukuma domin kara wayar dasu game da ayyukan cibiyar.

Ya ce cibiyar zata maida hankali ne wajen kasancewa cibiyar ilimin Alkur’ani ta duniya wadda zata dinga amfani da fasahar zamani da hada kimiyyar zamani da ilimin Alkur’ani cikin karatun Alkur’ani.

KU KARANTA: Jami’ar KHAIRUN Ta Karrama Yar Gombe Da Ta Yi Nasara a Musabaqar Alkur’ani ta Duniya

Shima a nasa jawabin shugaban cibiyar Barista Habibu Muhammad Dan-almajir Fagge ya ce cibiyar zata kawo sababbin hanyoyin koyar da manyan fannoni na Alkurani da kuma rubuce-rubuce a fannoni da suka shafi alkurani mai girma domin baiwa makarantasa dama a fannoni daban-daban kamar yadda kowanne bangare na ilimi suke gudanarwa don cigabansu.

Dan-almajir ya kara da cewar cibiyar zata dinga bibiyar tsangayu da rubuce-rubuce da shugabannin tsangayu sukayi a fannoni ilimi da dama.

Da yake tsokaci akan mihimmanci samar da cibiyar shugaban dakin karatu na jami’ar Malam Naziru Muhammad ya ce a shirye suka wajen tallafawa makaranta alkurani da adana bayanai da suka rubuta domin a buga shi da kuma nazari akansa da nufin amfanin alummar baki daya.

Mahaddata Alkur’ani daga kananan hukumomi jihar Kano 44 ne suka halarci taron wanda suka bayyana farin cikinsu bisa samar da cibiyar a Jami’ar ta KHAIRUN.

A karshe mahalarta taron sunyi addu’a ga marigayi Khalifa sheikh Isyaku Rabiu bisa gagarumar gudunmawa da ya baiwa Alkur’ani da kuma makarantansa a fadin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *