Jami’an ‘yan sanda dauke da manyan makamai sun rufe fadar mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da Takaita Zirga-zirga a Fadar.
Jami’an tsaron sun mamaye fadar ne tun da karfe 6 na safiyar ranar Juma’a, wanda hakan ya sa suka hana Sarkin fitowa daga fadar.
An lura da cewa ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya sun isa fadar inda suka dauki matakai masu muhimmanci a kewayen gidan Sarkin.
Majiyoyi sun ce Sarkin a kwanakin baya ya nada Dan sa sarautar Wanban Kano inda a yau aka shirya rakashi zuwa Bichi a matsayin hakimin Bichi, amma bai samu damar yin hakan ba saboda tsananin tsaro a fadar.
Kazalika majiyar ta bayyana cewa Sarkin ya shirya wani taro da malamai da masana tattalin arziki domin tattaunawa kan kudurin dokar sake fasalin haraji.
Sai dai tura jami’an tsaro ya hana gudanar da taron.
Sai dai a lokacin da ake hada wannan rahoto, Sarkin ya fito bakin babban fada tare da mukarrabansa a harabar harabar gidan inda ya saba gudanar da bukukuwa na gargajiya a lokacin bukukuwan Sallah.
Sanusi da mukarrabansa sun fito daga fadar cikin farin ciki da shagalin bindigu, da gaisuwar bangirma na gargajiya, da murna daga dimbin ’yan uwa da suka taru.