• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zan Haramta Wa Duk Yaran Da Aka Haifa A Amurka Izinin Zama Yan Kasa — Donald Trump

BySani Magaji Garko

Dec 9, 2024

Zababban shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce idan aka Rantsar da shi shugabancin kasar zai hana dukkan yaran da aka haifa a kasar Izinin zama yan Kasa.

Trump ya bayyana hakan ne a wata da yayi da Kamfanin Dillancin labarai na NBC.

Trump ya kuma jaddada alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe ciki har da batun sanya haraji a kan kayayyakin da manyan kasashe abokan kasuwancin kasar Amurka.

KU KARANTA: Yan Sanda a Amurka Na Shirin Kama Donald Trump

Koda aka tambayeshi batun kakabawa ma’aikata haraji, Mr Trump ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na NBC cewa shi ba zai ce komai ba a kan haka.

Cikin tattaunawar da aka da shi ta farko tun bayan samun nasara a zaben watan da ya gabata, Mr Trump, ya kara yin barazana akan ficewar kasarsa daga kungiyar tsaro ta NATO, muddin kasashe mambobin kungiyar suka gaza biyan kudadensu sannan kuma ya ce zai kara azama wajen mayar da ‘yanci ranin da basu da takardu zuwa kasashensu.

Kazalika cikin hirar da aka yi dashi, sabon shugaban na Amurka, ya ce zai kawo karshen ba wa yaran da aka haifa a kasar takardar shaidar zama ‘yan kasa.

Ya kuma ce ba zai rage kudin da ake tallafawa al’umma ko kuma sanya takunkumi a kan batun zubar da ciki.

Wani bincike da wata Kungiya tayi a jihar Pennsylvania ta kasar ta Amurka ta yi ya nuna cewa yanzu akwai yara miliyan 4.7 a kasar wanda dukkanin su Iyayen ba haifaffun Amurka ba ne kuma ana ganin zasu iya zarta haka nan da shekara ta 2050.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *