Karamin ministan man fetir da Iskar Gas Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo ya yabawa kamfanin Kula da albarakun man fetir na kasa NNPC bisa nasarar aiwatar da manufofin shugaban kasa ta hanyar samar da ayyuka masu tasiri ga ‘yan kasa.
Katafaren aikin guda ne cikin ire iren ayyuka samar da wutar lantarki na gaggawa dake Maiduguri (MEPP) wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar domin amfanar ‘yan kasa.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar samar da lantarkin ranar Asabar, 14 ga watan Disamba, 2024.
KU KARANTA: Kamfanin NNPCL Ya Kara Farashin Man Fetir
Ministan wanda ya samu rakiyar shugaban rukunin kamfanin NNPC Ltd., Mele Kolo Kyari, da mataimakin shugaban kasa, da sauran masu ruwa da tsaki na kamfanin NNPC, ya ce ayyukan suna tafiya yadda aka tsare bisa namijin kokarin NNPC.
Ita dai cibiyar samar da lantarkin MEPP wani aikin hadakar wutar lantarki ne mai karfin megawatt 50 da aka kaddamar a ranar 2 ga Maris, 2023.
Rahotonni sunce tuni an riga an kammala aikin 32MW na aikin kuma tuni ya fara aiki, yayin da sauran Megawatt 18MW zai fara aiki cikin shekarar 2025 dake karatowa.