Gidauniyar Hajiya Zainab Ahmed Suleiman ta fara aikin gina cibiyar koyar karatu da sana’o’i Kyauta ga marayu da masu karamin karfi a Kauyen Ruwantsa dake mazabar Kore cikin yankin karamar hukumar Danbatta dake jihar Kano.
Shugaba kuma mamallakiyar gidauniyar Hajiya Zainab Ahmed Suleiman ce ta jagoranci masu ruwa da tsaki don duba filin gami da daukar bayanai da za’ayi amfani da su wajen gina cibiyar wacce zata rika horar da mata da matasa sana’o’in dogaro da kai a garin na Ruwantsa.
Zainab Suleiman wacce itace garkuwar Marayun karamar hukumar Danbatta ta ce gina cibiyar ya zama wajibi don a sami gurin da za’a rika koyar da mata da matasa sana’o’in dogaro da kai da kuma tallafawa iyalai la’akari da halin matsin rayuwa da kuma kokarin da ake na ganin mata sun fara bada gudun mowa don tallafawa iyalinsu maimakon dogaro kacokan ga miji ya dauki nauyin iyali baki daya.
KU KARANTA:
“A cibiyar zamu gina gurin koyar da sana’o’i da masallacin don cigaban harkokin addinin musulunci da kuma jawo ruwa a gurin don bawa mutane sadaqatuj-jariya, musamman don tallafawa al’umma da cigaban garin Ruwantsa,” inji Zainab.
“Zamu koyawa mata a wannan gari sana’o’i kamar dinki, hada takalma da jakankuna da hada sabulu da man shafawa abubuwan da baza a rasa ba musamman wadanda zasu iya siyarwa a yankunansu,” inji Garkuwar Marayun.
“Sannan zamu dora mata a shirin adashin gata ta yadda zasu rika kasuwanci tsakaninsu, sannan karku manta munfi shekaru 10 muna rigakafi a karamar hukumar Danbatta, to zamu cigaba da koya musu yadda zasu rika kula da lafiyar iyalansu, su kuma su tabbatar suna bin mazajensu sau da kafa da kuma yi musu biyayya saboda kar mace taga ta fara samun kudi ta fara raina mijinta,” inji Zainab.
Shugabar gidauniyar ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki dama al’umma da su himmatu wajen tallafawa yunkurin cibiyoyi da gidauniyar ta Zainab Ahmed Suleiman don hada hanu da nufin cigaban yankunan karkara a fadin arewacin Nigeriya wanda shine yankin da ya zamo koma-baya a kasar nan.
Abbas Magaji Ruwantsa, shine Dagacin garin Ruwantsa cikin mazabar Kore a Danbatta ya ce masarautar yankin zata cigaba da tallafawa dukkan yunkurin cigaban mutanen yankin.
“Duk mutumin da zai dauki zunzurutun kudinsa ya sayi filin a garin nan ya kuma kawo kudin da za’a sayi kayan aiki ba karamin mai son cigaban al’umma bane, saboda haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma suma su tallafa don samun nasarar,” inji Abbas.
Dagacin yayi kira shugabannin al’umma da yan siyasa da masu hanu da shuni da su tallafawa yunkurin gidauniyar Zainab Ahmed Suleiman don tallafawa mata da matasan yankin.
Abbas Magaji ya kuma bada tabbacin bibiyar dukkan mahukuntan yankin domin su tabbafawa garin Ruwantsa dama al’ummata.