• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Majalisar Malamai Ta Kano Ta Sasanta Rikicin Shugabanci a Masallacin Sahaba Na Kundila

BySani Magaji Garko

Feb 19, 2025

Shugaban Majalisar Malamai ta kasa Sheikh Ibrahim Khalil ya sanar da warware takaddamar shugabancin da ta shafi Limamin Masallacin Jami’ur Rahman da ke Kundila, Kano.

Majalisar ta yanke hukuncin cewa Sheikh Muhammad Bin Usman, wanda shi ne babban limamin tsohon masallacin, ya koma masallacin Sahaba domin ci gaba da gudanar da limanci da koyarwa, kuma an cimma wannan ne bayan tattaunawa da bangarorin biyu da abin ya shafa.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron majalisar, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa sauran bangaren karkashin jagorancin Mai Kifi, za su ci gaba da rike shugabancin sabon masallacin, Jami’ur Rahman.

KU KARANTA: Zamu Duba Yiwuwar Kara Alawus Din Limamai Da Ladanai — Shugaban K/H Dala

Sannan kuma ya tabbatar da cewa Sheikh Muhammad Bin Usman ya amince da kudurin kuma zai ci gaba da aikinsa a Masallacin Sahaba.

Shugaban karamar hukumar ya kuma yabawa hukumomin tsaro bisa rawar da suka taka wajen sasanta rikicin da ya janyo cece-kuce tsakanin malamai da jama’a, ba wai a Kano kadai ba, har ma a fadin Najeriya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *