• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Sarkin Kano Ya Halarci Faretin Cikar Kasar Gambia Shekaru 60 Da Samun Yancin Kai

BySani Magaji Garko

Feb 19, 2025

DAGA: SANI IDRIS MAI-WAYA, KANO

Mai Martaba Sarkin Kano Na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya bayyana Shugabanci a matsayin Wani tsani na Ciyar da Al’umma Gaba.

Mai Martaba Sarkin Kano ya bayyana hakan ne a wajen bikin Faretin Cikar kasar Gambia shekaru 60 da Samun yancin kan kasar ta Gambia a Banjul, babban birnin kasar.

An dai gayyacin Sarkin Kanon Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu a matsayin babban bako na musamman a kasar ta Gambia dan Taya Al’umma bikin murnar Cika Shekaru 60 da Samun yancin Kai.

KU KARANTA: Muna Rokon Al’umma Su Guji Ta Da Hankali a Lokacin Zabe — Sarkin Kano

Da yake Jawabi tun da farko a gurin Taron, Shugaban Kasar Gambia Adama Barrow ya yabawa Sarkin Kano bisa Amsa gayyatar da sukayi masa.

Haka Kuma Barrow yayi Fatan Alkhairi Ga Sarkin da kuma Shugabannin Kasashen Guinea, da Senegal, sai Jakadun Kasashen daban daban Har ma da Shugabannin Addinai da Yan kasuwa da suka samu damar Halarta Taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *