DAGA: SANI IDRIS MAI-WAYA, KANO
An bayyana kyakyawar Alaka tsakanin Masarautu a Matsayin Wata Hanya daka Iya Samar da Cigaba a Tsakanin Al’umma.
Sarkin Bade, daga Jihar Kaduna, Daliel Lemson Shine ya bayyana hakan yayin da ya Kai ziyarar nuna mubaya’a ga Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu a Fadarsa.
Sarkin yayi Addu’a ta musamman ga Sarkin Kano tare da Fatan Alkhairi Ga Mai Martaban Kan yadda yake gudanar da Ayyukan Cigaba ga Rayuwar Al’umma.
KU KARANTA: Sarkin Kano Ya Halarci Faretin Cikar Kasar Gambia Shekaru 60 Da Samun Yancin Kai
Sarkin Bade, Daliel Lemson na daya daga cikin Sarakunan da Suka zo jihar Kano dan nuna Goyon Bayan Su Ga Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu.
A nasa Jawabin Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya yaba da wannan Ziyarar da Sarkin na Bade, ya Kawo masa.
Haka Kuma Sarkin Kanon Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya ce a Koda yaushe kofar Masarautar Kano a bude take wajen bada gudummawar dan Cigaba Al’umma.
Yayin Ziyarar Sarkin Baden na tare da Ayarin Jami’an Masarautar sa daga Jihar Kaduna da sukayi Masa Rakiya.