• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ku Bada Zakka Don Inganta Dukiyarku, Tallafawa Mabuqata, Shaik Habibu Dan-almajiri Ya Roki Mawadawa, Gwamnatoci

BySani Magaji Garko

Feb 20, 2025

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Sabon shugaban hukumar zakka da Hubusi ta jihar Kano sheikh Barista Habibu Muhammad Dan almajir ya bukaci mawadata da gwamnatoci da su bada Zakka don Inganta Dukiyarku da kuma tallafawa Mabuqata da masu karamin karfi.

Shugaban ya kuma bukaci gwamnatoci da kungiyoyi da dai-daikun al’umma da suke bada Zakka da su bawa hukumar Zakka da Hubusi hadin kan da ya dace domin gudanarda ayyukanta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Barista Dan almajir a watattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER ya tunatar da al’umma cewa zakka rukuni ce daga cikin rukunun addinin musulunci domin bayan tauhidi da sallah sai kuma zakka, adan haka yake bukatar mutane dasu basu cikakken hadin kai domin gudanarda aikin kamar yadda mai girma gwamna Alhaji Abba kabir ya basu amanar gudanarda aikinsu ba tare da nuna bambanci ba.

KU KARANTA: Sabon Shugaban Hukumar Zakka Da Hubusi Ya Kama Aiki

Ya ce kofar hukamar a bude take ga duk wanda yake bukatar zai rabawa alummarsa zakka a duk inda yake daya gayyato jami’an hukumar da suzo su Raba masa ko kuma su Sheda yadda Rabon yake gudana ko ya Raba gida biyu ya baiwa hukumar kaso daya suma suje su baiwa mutane domin suyi masa sheda a duniya da lahira.

Sheikh Dan àlmajiri ya ce hukumar zakka an samar da ita ne domin karbar zakka daga hannun mawadata da suke cikin alumma da kuma rabata ga mabukata wanda hakan yake tallafawa mutuka wajen rage talauci da fatara da kuma sanya kauna a tsakanin allumma.

Ya ce za suyi iya kokarinmu duk abinda aka kaiwa hukumar a matsayin zakka su rabata ga mabukata ba tare da mun tauye komai ba a ko ina a fadin jihar Kano.

Ya ce a yanxu Nisabin zakka ta kudi ya kai kimanin Naira Miliyan goma sha daya da dubu dari bakwai da chasain da shida da dari biyu da Arbain 11,796,240, sai kuma zakka kayan Noma da dabbobo da sauransu.

Sheik Dan almajir ya ce hukumar zata dinga fitar da bayanan a game da zakka domin kara tunatar da alumma ta kafafan yada labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *