• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Kashe Naira Miliyan 105 Don Bunkasa Ilimi a Karamar Hukumar Dala — Surajo Imam

BySani Magaji Garko

Feb 21, 2025

DAGA: SANI IDRIS MAI-WAYA, KANO

Karamar hukumar Dala ta ce zata kashe sama da naira miliyan 105 don inganta harkokin Ilimi a fadin yankin.

Shugaban karamar hukumar ta Dala Alhaji Surajo Ibrahim Imam shine ya bayyana hakan yayin daya Karbi bakuncin kungiyar malaman makaranta NUT reshen karamar hukumar Dala a ofishin sa.

Shugaban ya ce za’a kashe kudin ne wajen gyaran Azuzuwa da samar da kayan koyo da koyarwa da inganta walwalar malamai la’akari da muhimmancin da malaman ke da shi wajen samar da ilimi ga dalibai.

KU KARANTA: Zamu Duba Yiwuwar Kara Alawus Din Limamai Da Ladanai — Shugaban K/H Dala

Ya kara da cewar gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na bawa harkar ilimi kulawar data kamata musamman a karamar hukumar ta Dala.

“A wannan karon Gwamnan ya Sahalewa karamar hukumar Dala dan gyara sashin kula da ilimi na yankin wanda ake sa ran za’a kashe sama da naira miliyan 105 don cimma burin da aka sanya a gaba,” inji Imam.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar malaman makarantar ta (NUT) Malam Yahaya Ramadan ya yaba da yadda shugaban karamar hukumar Dala ke bawa bangaren ilimi kulawar data kamata

Malam Yahaya Ramadan ya kuma ce kungiyar tana Mai kara mika godiya ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa karin girman ga malamai da kuma samar da kayan makaranta (uniform) ga dalibai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *