• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An Ga Watan Ramadan A Nigeriya

BySani Magaji Garko

Feb 28, 2025

Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan.

Cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Fara Duban Jinjirin Watan Ramadan

Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446.

Tuni dai hukumomin Saudiyya suka sanar da ganin watan a ƙasar, inda suka ayyana gobe Asabar a matsayin ɗaya ga watan Ramadan a Saudiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *