• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

A hir Din Kungiyar CAN Da Yiwa Musulmi Kutse A Addininsu — Yusuf Dingyadi 

BySani Magaji Garko

Mar 4, 2025

DAGA: ABDULLAHI ALHASSAN, KADUNA

Fitaccen ɗan jarida kuma ɗan siyasa, Malam Yusuf Abubakar Dingyaɗi ya koka da yadda Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) take yi wa Musulmi kutse a kan ‘yancinsu.

Dingyadi ya ja kunnen kungiyar CAN da ta Dena shiga sabgar da babu Ruwanta kuma ba ta da hurumi a ciki.

Idan za’a iya tunawa kungiyar CAN ta yi sukan yadda wasu jihohin Nigeriya ciki harda Kano da Bauchi da Kebbi suka yi hutun Makarantun firamare da sikandire kwana guda kafin fara Azumin watan Ramadan.

KU KARANTA: Dungurawa Bashi Da Hurumin Dakatar Da Ni ko Kabiru, Sanata Doguwa Ne Halastaccen Shugaban NNPP a Kano — Kawu Sumaila

Ya ce hakan ya faru ne sanadiyar rashin haɗin kai na Musulmin Najeriya da yadda rarrabuwar kawunan Malamai take ƙara ta’azzara, suna cin zarafin junansu.

A wata takardar ƙorafi da ya aikawa manema labarai, Dingyaɗi, wanda shi ne Magayaƙin Garkuwan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce “Baki ɗaya yanzu ana ci gaba da wulaƙanta rinjayen Musulmi saboda ba mu da murya ɗaya mai ƙarfi.”

Ya ci gaba da cewa, “An yi amfani da siyasa don wargaza mana mutunci. Sai kuma son rai a shugabanni da ke amfani da ikonsu wajen cin zarafin wasu daga cikin shugabannin da suke da girma a fuskar al’umma.”

Malam Yusuf ya buƙaci al’ummar Musulmi da su haɗa kai domin kare mutunci da martabar kansu. Kamar yadda ya nemi ƙungiyar ta CAN da ta tsaya a matsayinta, ta daina shisshigi ga lamarin da ya shafi al’ummar Musulmi, domin a zauna lafiya da mutunta juna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *