Kungiyar ma’aikatan Radiyo da Talabijin da Dakunan Wasannin kwaikwayo (RATTAWU) ta kasa ta bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta tallafa domin samar mata ofis na Din-Din-Din don cigaban ‘ya’yan ta.
Shugaban kungiyar na kasa reshen jihar Kano Alhaji Babangida Mahmoud Abiyamusu ne ya bukaci haka ta hanun kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya lokacin taron baiwa ‘ya’yan kungiyar tallafin kazar Sallah domin Jin dadinsu, taron da ya gidana sakatariyar kungiyar jiya Juma’a.
Shugaban ya roki gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf da ya tallafa domin samar musu da babban ofis don barin inda suke haya a yanzu.
KU KARANTA: IPAC Tayi Allah Wadai Da Kalaman Batanci Da Yan Siyasa Ke Yiwa Juna A Kano
Babangida Abiyamusu ya ce a lokatuna baya kungiyar na shirya shan-ruwa ga ‘ya’yan ta don hada dakon zumuncin musamman a lokacin Azumin watan Ramadan, Yana mai cewa da ya karbi ragamar gudanar da Kungiyar sai ya ga dacewa bawa ‘ya’yan kungiyar tallafin kazar Sallah wanda su da iyalansu zasu amfana maimakon su kadai a lokacin shan-ruwa.
“A baya da nazo naga ana shirya shan-ruwa, amma sai na gano cewa idan ka kira mutum kace yazo shan ruwa shi kadai ne zai amfana, Kai wani ma bazai zo ba, sai nayi tunani maimakon haka a dunkule kudin da za’a kwashewa duk mutum daya a lokacin shan-ruwa ruwan a bashi su dab da Sallah, kaga kenan zai sayi kaza da sauran kayan kwalan da makulashe ya je gida shi da Iyalansa cikin annashuwa su ci,” inji Abiyamusu.
Shugaban ya kuma roki tallafin gwamnatin Jihar Kano a shirye-shiryen da suke na zuwa babban taron kungiyar na kasa da za’ayi a nan gaba kadan domin tsayar da daya daga cikin ‘yan kungiyar a nan Kano takarar wani mukami a zaben kungiyar na kasa da za’ayi.
A jawabinsa, kwamishinan ƴada labarai na Jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yabawa yayi bisa gayyatar da Kungiyar ta yi masa inda nan take ya bada naira miliyan daya (1,000,000.00) domin tallafawa ‘ya’yan kungiyar da tallafin kazar Sallar.
Dangane da koken ofis na din-din-din kuwa, kwamishinan ya bukaci su robuta don isar da shi ga gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf domin tallafawa ‘ya’yan kungiyar, yana mai cewa gwamna mai kishin mutanen da suke rajin cigaban al’umma ne.
Waiya ya kuma bada tabbacin ma’aikatar yada labarai zata cigaba da aiki da Kungiyar kusa-da-kusa don cigaban al’ummar Jihar Kano.