Daya daga cikin kwararru a nan Kano Alhaji Salisu Salisu Umar ya ce matakin da gwamnatin Jihar Kano da hukumar ta ce fina-finai da Dab’i suka dauka na soke ‘Kauyawa Day’ a bukukuwan daurin Aure a jihar Kano kuskure ne, daukar matakin koma baya ne ga cigaban walwalar Al’umma.
Ya ce kamata yayi gwamnatin Jihar Kano ta dauki gabarar tsaftace tsarin don Nishadantar da al’umma maimakon soke tsarin.
Salisu Salisu Umar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Kano ranar Alhamis.
READ ALSO: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shirin Labarina, Dadin Kowa, Da Wasu Guda 20
A cewarsa, hana ko dakatar da Kauyawa Day da Dakatar da wasu shirye-shirye masu dogon zango guda 22 da hukumar ta ce fina-finai ta yi zai Kara saka mutanen cikin takura domin da ire-iren wadannan shirye-shiryen ne mutane suke samun Nishadin kuma ya zama musu masalahar wadansu damuwowi da suke fuskanta.
“Tunda Abba El-Mustapha ya zo hukumar ta ce fina-finai babu wani tsari da ya samar na bunkasa Nishadi ko samar da kudaden shiga ga gwamnatin Jiha, maimakon haka sai ya buge da dakatarwa da Soke hanyoyin walwalar Al’umma, Kai wadannan fina-finan da yake dakatarwa tun yana cikin Yan film ake yinsu, kuma bai taba fitowa ya kalubalanci tsarin ba sai yanzu da ya sami dama ?,” Inji S S Umar.
“Baza ka iya kididdige mutanen da suke da hawan Jini a jihar Kano ba, baza ka iya kididdige masu cutar damuwa ba (Depression) musamman matan Aure ba, ba za ka iya kididdige mutanen da suke fama da shaye-shaye sanadiyyar rashin guraren shakatawa ba, saboda haka duk wadannan matakan da gwamnatin Kano da Abba El-Mustapha suke dauka rusa cigaban al’umma ne, kuma zama su iya kawo matsalar tsaro,” inji Umar.
“Yanzu a jihar Kano babu wani guri da za’a iya kai yara kanana don shakatawa, babu gurin da aka warewa Matasa kawai kamar Yan Shekaru 20, 30, 40 don shakatawa ba, yanzu babu inda aka warewa Mayan Mutane kamar Yan Shekaru 40, 60 zuwa sama don su shakata ba, Dole a samu tarin masu cutar damuwa, gari kamar Kano babu ire-iren wadannan gurare, yakamata gwamnati ta samar aa tsari irin wannan,” inji Umar.
Kwararren ya shawarci gwamnatin Jihar Kano da ta samar da wata ma’aikata dungurungum wacce zata mayar da hankalin wajen cigaba da bunkasa walwalar Al’umma (Ministry of Happiness and social Development).
Ya shawarci gwamnatin Jihar Kano da ta Kago sabbin guraren shakatawa tare da gyara wadanda ake da su domin cigaban walwalar Al’umma Jihar.