• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An Kashe Wani Mutum Saboda Ya Je Zance Wajen Budurwarsa a Kano

BySani Magaji Garko

May 25, 2025

Rikici tsakanin matasa a kauyukan Faruruwa da Tarandai ya yi sanadin kashe wani saurayi a karamar hukumar Takai da ke Jihar Kano.

Bayanai da Dan jarida Mai bibiyar harkokin tsaro a yankin Tafkin chadi da kasashen Afirka ta yamma Zagazola Makama ya samu sun tabbatar da cewa rikicin ya faru ne a ranar 23 ga watan Mayun 2025 da misalin Karfe 7:45 na yamma.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne a ranar Kasuwar kauyukan biyu wanda ya yi sanadin Kone shugana na wucin gadi a kasuwar.

KU KARANTA: Ayyukan Cigaban Al’umma: An Karrama Shugaban Karamar Hukumar Ghari a Kano

Kwarya-kwaryar binciken da aka gudanar sun tabbatar da cewa an kashe matashin mai suna Sani Yunusa dan shekaru 28 dan asalin Kauyen Toho Diribo saboda ya je wajen budurwarsa a kauyen Tarandai dukka a karamar hukumar Takai.

“An kaiwa saurayin hari da adduna da sanduna lokacin da yake dawowa daga zance,” inji wasu bayanai.

To Amma an tabbatar da cewa tuni jami’an tsaro suka shiga tsakanin bangarorin biyu tare da maido da zaman lafiya.

Rundunar Yan Sandan ta ce tana cigaba da gudanar da bincike don kama wadanda ke da hanu a lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *