• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Dalilin Da Yasa Hukumomi Suka Hana Sheikh Ahmed Gumi Shiga Kasar Saudi Arabia

BySani Magaji Garko

May 26, 2025

Hukumomin kula da shige da fice na kasar Saudi Arabia sun hana shahararren Malamin Addinin musulunci dan Nigeriya Sheik Ahmed Abubakar Mahmoud Gumi shiga Kasar duk kuwa da Bashi Biza da aka yi.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya ce: “Bisa wasu dalilai da suka shafi ra’ayina game da siyasar duniya, hukumomin Saudiyya ba sa son in kasance a aikin Hajji duk da sun ba ni biza.”

Ya ce hukumomin Najeriya sun sha alwashin tuntuɓar ƙasar Saudiyya domin jin dalilin hana shi shiga ƙasar.

KU KARANTA: Binciki Masu Daukar Bidiyon A. A. Rufa’I, Wani Lauya Ya Bukaci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

To Amma Jaridar GLOBAL TRACKER a bayanan da ta tattaro sun tabbatar da cewa hana Sheik Gumi shiga Saudi Arabia na da alaka da kalamansa da yayi game da ziyarar shugaban Amurka Donald Trump zuwa kasashen Saudi Arabia da Qatar da kuma Hadaddiyar daular Larabawa wato UAE.

A karatun da yayi, Gumi ya caccaki kasashen Larabawa musamman Saudi Arabia bisa yadda suka kulla yarjejeniyar kasuwanci ta Makudan kudade da Amurka, a dai-dai lokacin da Amurkan ke tallafawa Isra’ila tana kasashen Yan uwansu Larabawa a zirin Gaza.

GLOBAL TRACKER sashen Turanci ya rawaito yadda a ziyarar da Trump ya kai Saudi Arabia, Riyadh da Washington suka kulla yarjejeniyar kasuwanci ta dala Biliyan dari da arba’in da Biyu ($142,000,000,000.00).

“Yau muke ji a labaru shugaban kasar Amurka Donald Trump ya na cewa Turawan dake ke South Africa wai ana kuntata musu, ana kwace musu filaye da gonakinsu saboda haka suke neman Mafaka a bude musu Amurka su yi hijira, abinda ya ce ai ana yi musu kisan gilla, wai ‘Genocide’, wai bakake na ‘Genocide’ suna kashe farare a South Africa, shugaban Amurka ke fadar haka, sai gashi ya tara shugabanni Larabawa suna Miki mishi makudan kudaden da Hankali bai dauka, wai ya je yayi ‘investment’ da su a Amurka, makudan kudi fa suke bashi, a lokacin da yake taimakawa Isra’ila take kisan gilla na gaske wa musulmi, wanda south Africa tun tuni ta ce kisan gilla ne kuma ta kai kotun Duniya, kuma kotun Duniya ta ce hujjojin da aka kai sun Isa a tabbatar da kisan kiyashi saboda haka a Kamo Netanyahu a kawo shi gaban kotu,” inji Sheik Gumi.

“Amma ga kasashen Larabawa sun taru suna marhabun da Trump, suna dari-dari da shi, to akwai wani Abu da suka hadu akansa, dukkan idan kun duba sarakunan gargajiya ne ke mulkin wadannan kasashen, domin kowa kujerarsa yake karewa bayason a tayar masa da rigima a kasarsa saboda mulkin da yake. To ko wanda ba sarakunan bane ke mulkin, duk haka suke matsorata ne……. Balarabe ya raina kowa amma banda Bature, indan Bature ya zo ai Balarabe makyarkyata yake…… Kalli mutanen nan Yan Taliban, shekaru 20 sukayi suna yaki da turawa da Yan faransa, amma sukayi hakuri, kuma sukayi nasara, Amma Balarabe kana rike da Makka da Madina kuma kana tsoro…,” Inji Gumi.

Abin Jira dai shine yadda gwamnatin tarayyar Nigeriya za mayar da martani da bibiyar da hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON za tayi domin Sheik Gumi ya na cikin mutanen da NAHCON din ta biyawa aikin hajjin bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *