Al’ummar garin Rano dake Jihar Kano sun yiwa babban Baturen Yan Sandan yankin (DPO) dukan kawo wuka wanda ya yi sanadin mutuwarsa sakamakon zargin Yan sanda da kama wani bakanike gami da yi masa dukan-tsiya har ya mutu.
Tunda farko, al’ummar garin sun zargi Yan sanda da yiwa wani bakaniken babur mai suna Abdullahi Musa dukan tsiya sakamakon zargin sa da tukin ganganci.
Bayan anyi ma Abdullahi Musa duka jikinsa ya yi tsami lamarin da ya sa aka Kai shi Asibiti kafin daga bisani ya rasu.
KU KARANTA: Hukumar Kare Hakkin Mai Siye Da Siyarwa Ta Kama Lalatattun Kaya Na Sama Da Miliyan 400 a Kano
Lamarin ne ya sa al’ummar garin suka harzuka gami da kaiwa Ofishin Yan sandan gari hari tare da Kona wani bangare da kuma Kone motoci biyu da fasa wasu da dama.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar Yan Sandan Jihar Kano ya tabbatar da Lamarin cikin wata sanarwa da ya aikewa manama labarai a Kano ranar Litinin.
“Bayan mutuwar bakaniken ne mutanen yankin suka kaiwa Ofishin Yan sandan garin Rano hari inda suka lalata motoci goma (10) gami da yiwa DPO munanan rauni. An Kai DPO Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano inda daga bisani ya rasu,” inji Kiyawa.
Ya ce ya zuwa yanzu an kama mutane 27 da ake zargi da hanu a lamarin.
Kiyawa ya ce kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano Ibrahim Bakori ya ziyarci garin inda ya yiwa Sarkin Rano da Iyalan wanda abin ya shafa ta’aziyya tare da bada umarnin gudanar da sahihin bincike.
Kwamishinan ya bada tabbacin yin gaskiya a binciken domin gano musabbabin afkuwar lamarin tare da gujewa faruwar lamarin a nan gaba.