Kasar Spain Da Ireland za su kakabawa kasar Isra’ila takunkumi sakamakon kisan gillar da ta ke yiwa Falasdinawa a yakin Gaza.
Ministan harkokin wajen Spain Manuel Albares Bueno ya ce dole sai kasar sa ta dauki matakin Kakabawa Isra’ila takunkumi don kawo ƙarshen yakin Gaza wanda nauyi ne da ya rataya a kansu.
Ita ma, kasar Ireland ta ce zata gabatar da kudiri a gaban majalisar dokokin kasar domin dakatar da dukkan huddar Kasuwanci da kamfanonin Isra’ila da suke ‘West Bank’, wanda sune kasashe na farko daga tarayyar Turai da za su dauki matakin.
KU KARANTA: Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yakin Gaza: An Cigaba Da Muyasar Firsunoni Tsakanin Isra’ila da Hamas
“Dokar idan majalisar ta amince da ita zata umarci dakatar da dukkan huddar Kasuwanci da kamfanonin Isra’ila wanda shine zai zama martani ga lefukan yaki da Isra’ila ke yi yanzu haka a Gaza,” inji Ministan harkokin wajen Ireland.
“Hana ketarar da abinci zuwa Gaza wanda hakan yake janyo mutuwar kananan Yara lefi ne babba, kuma abin kunya duniya ta kasa yin komai a Kai,” inji Ministan.
Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da kasashe 11 suka yiwa jakadunsu daga Isra’ila kiranye tare da dakatar da huldar jakadanci da Tel Aviv din.
Kasashen sune Jordan, Bahrain, Turkey, Bolivia, Colombia, Honduras, Chile, Belize, Brazil, South Africa da kuma Chadi.