• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Hukumar Zakka Da Hubusi Ta Ziyarci Da Tallafawa ‘Yan Wasan Kano Da Sukayi Hatsari

BySani Magaji Garko

Jun 5, 2025

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Hukumar Zakka da hubusi ta jihar Kano ta kai ziyarar jaje da kuma ta’aziyya ga wadanda ibtilain hadarin mota ya hada dasu bayan sun halarci gasar wasanin motsa jiki ta Kasa da aka gudanar a jihar Osun, inda 22 daga cikinsu suka rasu yayin da wadansu kuma suke kwance a Asibitin murtala dake cikin Birnin Kano suna karbar magani.

Shugaban hukumar Barrista Habibu Muhammad Dan-almajiri wanda kwamishina na 1 a hukamar sheikh Nafiu Umar Harazumi ya wakilta ne ya bayyana ga wakilin GLOBAL TRACKER.

Shugaban ya ce sun kai ziyarar ne domin su jajantawa wadanda suka samu raunuka a yayin hadarin motar, da kuma mika ta aziyya ga daukacin alummar jihar Kano bisa babban rashin da aka yi.

KU KARANTA: Kungiyar Masu Dillancin Filaye a Kano Ta Gudanar Da Taron Tsaftace Ayyukanta

Sheikh Harazimi ya ce daga cikin ayyukan hukamar zakka da hubusi akwai tallafawa wadanda suka gamu da wata jarrabawa kasancewa addinin musulunci yayi umarni da taimako a tsakanin allumma ta fannoni da dama.

Shima a nasa jawabin shugaban Asibitin kwararru na murtala Muhammad Dakta Hussain ya yabawa shugabanini hukumar zakka da Hubusi ta jihar Kano bisa ziyarar jaje da suka kawo musu da kuma tallafi da suka baiwa wadanda ibtilain ya rutsa dasu.

Khatimu Hussain da Aliyu na daga cikin wadanda suke kwance a Asibitin sun bayyan farin cikinsu bisa tallafi da kuma ziyarar dubiya da aka musu inda suka ce gwamnati tana basu kulawar da ta dace.

Taron ya samu halartar shugabanin hukumar zakka da Hubusi ta jihar Kano da suka hadarda Sheik Arabi Tudun Nufawa da kuma daraktan gudanarwa da sauran shugabanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *