• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

DA DUMI-DUMI: Isra’ila Na Shirin Kai Hari Kan Nukiliyar Iran, Tehran Ta Yi Alkawarin Mummunar Ramuwar Gayya

BySani Magaji Garko

Jun 9, 2025

Kasar Isra’ila na shirin kai hare-hare kan guraren makaman Nukiliyar kasar Iran.

Haka ma, Iran ta yi alkawarin mummunar ramuwar gayya ta hanyar lalata dukkan guraren da ake ajiya ko kera nukiliyar Isra’ila.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Iran ta yi watsi da yarjejeniyar da Amurka ta aike mata, tana mai cewa babu komai sai rashin adalci da zalunci.

KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: An Harbe Daya Daga Cikin Kwararrun Malaman Iran

A kunshin yarjejeniyar da Iran ta yadda da shi dai ya amince Tehran ta cigaba da habaka nukiliyarta tare kuma da rusa na Isra’ila, yarjejeniyar da ake ganin bata da ko da fuskar kallo ballatana amincewa da ita a Washington.

“Matukar Isra’ila ta yi kuskuren kaiwa nukiliyarmu hari, to zamu tabbatar mun lalata dukkan wani guri da yake dauke da bayanai ko nukiliyar Isra’ila wanda ake ta boye su, amma yanzu duk mun san inda suke kuma zamu lalata su,” inji shugaban majalisar tsaron Iran.

“Ko a yau dinnan Isra’ila na cigaba da shirye-shiryen kai hari zuwa Iran musamman guraren nukiliyarta,” inji Israel — Channel 12.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar kula da kerawa da kuma yada fasahar nukiliya ta Duniya Rafael Grossing ya ce, Iran ta sa ce wani kaso mai yawa na bayanan nukiliyar Isra’ila.

“Mai yuwawa an sace bayanan ne daga cibiyar ‘Soreq’ ta Isra’ila,” inji Grossi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *