A tattaunawar da sukayi ta wayar tarho, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gayawa Fire Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa “Babu maganar yaki Da Iran”.
Kalaman Trump na zuwa ne bayan da Netanyahu ya bukaci Amurka ta dakatar da dukkan wata tattaunawa da Iran, ita kuma Isra’ila na shirin kai hare-hare kan dukkan guraren makaman nukiliyar Tehran din.
“Bazan amince maka ka kaiwa Nukiliyar Iran hari a yanzu, ko kuma nan kusa-kusa ba, kuma Ina baka shawara ka fada tare da aiwatar da dena tattaunawa don kaiwa Iran hari,” Trump ya gayawa Netanyahu.
“Iran ta dauki zafi game da wannan tattaunawa, kuma tana yin gatse ko fadar bakaken maganganu game da wannan shirin, Amma duk da haka a shirye muke mu zauna da su don cigaba da tattaunawa,” inji shugaban Amurka.