Vishwash Kumar Ramesh, shine mutum daya tilo da ya tsira daga hatsarin jirgin ‘Air India mai dauke da mutane 242 wanda da farko aka tsara zai sauka da misalin Karfe 6:25pm wanda yayi dai-dai da (17:25GMT).
Babban likitan da ya duba wanda ya tsiran ya ce Kumar Ramesh ya samu raunuka a ko Ina a jikinsa, amma jikin yana karbar kulawar da ake masa.
Jirgin samfurin Boeing 787 wanda yake dauke da ‘yan kasar India 169 da ‘Yan Birtaniya 53 da 1 Dan asalin kasar Canada da kuma mutane 7 ‘yan Portugal ya fado ne a garin Ahmedabad Jim kadan bayan ya tashi.
KU KARANTA: NAFDAC Ta Yi Gargaɗi Kan Jabun Maganin Malaria
Faruwar lamarin ke da wuya shugabanni kasashen Duniya suka fara mika ta’aziyyar su ga kasar India da kuma sauran kasashen da wandanda ke cikin jirgin suka fito.
Sakatare janar na majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bakin cikinsa dagane da hatsarin inda ya Mika ta’aziyya ga Iyalan wanda abun ya shafa.
Sakataren harkokin Amurka Marco Rubio da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da Firi Ministan Italy Giorgio duk sun mika ta’aziyyar su.
Sauran wandanda suka mika ta’aziyyar sun hadar da shugaban kasar Philippines Ferdinand Marcos Jr da Shehbaz Sharif, Firi Ministan Pakistan da shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Volodymir Zelenskyy na Ukraine da kuma Benjamin Netanyahu na Isra’ila.