Majalisar kula da huldar ‘yan Amurka da Musulmi a Duniya “Council on American– Islamic Relations (CAIR)” ta yi Allah wadai da kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa dukkan Al’ummar Birnin Tehran, babban birnin kasar Iran su fice don bawa Isra’ila dama kai hare-hare.
Cikin sanarwar da majalisar ta fitar ta ce Trump na kokarin yin kuskuren da tsohon shugaban Amurka George W. Bush ya yi lokacin da ya bawa sojojin kasar umarnin mamaye kasar Iraq.
“A wancan lokacin George W Bush ya yi ikirarin da babu hujja cewa kasar Iraq na kokarin kere makamin Nukiliya.”
KU KARANTA: ‘Babu Maganar Yaki Da Iran’, Trump Ya Gayawa Netanyahu
To Amma Jaridar GLOBAL TRACKER ta rawaito cewa wasu daga cikin ‘Yan shahada’un shugaban Amurka Donald Trump a majalisar dattawan Amurka sun kai kudirin dokar cewa dole shugaban ya nemi sahalewar majalisa kafin ya bada umarnin kaiwa kasar Iran hari.
‘Yar majalisa Thomas Massie wacce yar jam’iyar Republican ce kuma Yan shahada’un Trump ce ta kai kudirin.
Kudirin ya kuma umarci shugaba Trump ya dakatar da dukkan wani umarni na kaiwa Iran hari wanda ba majalisa ce ta amince da shi ba.