Hukumar Zakka ta Hubusi ta Jihar Kano hadin gwiwa da hukumar Shara’a da majalisar Malamai da ta Limaman Juma’a da kuma kungiyar ma’aikatan Zakka da Wakafi ta kasa sun amince da Naira dubu asirin (20,000.00) a matsayin mafi karancin Nisabin Sadakin Aure.
Haka kuma sun amince da Naira miliyan dari da hamsin (150,000,000.00) a matsayin Diyyar wanda ya kashe Rai bisa kuskure da kuma naira dubu Dari tara da tamanin da biyar (985,000.00) a matsayin Nisabin Zakka.
Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad, Malami a Jami’ar Bayero dake Kano kuma babban Sakataren kungiyar masu aikin Zakka da wakafi ta kasa ne ya bayyana hakan a jawabin bayan taro da hukumar Shara’a ta Jihar Kano da Takwararta ta Zakka da kungiyar Limaman masallatan juma’a da majalisar Malamai ta Jihar Kano da kungiyar ma’aikatan Zakka da wakafi ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar, taron wanda ya gudana a Kano a Alhamis din nan.
KU KARANTA: Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Rano
“Abubuwan da aka amince da su a wannan taro sune kamar haka;
1. Taron ya amince da amfani da Durham a matsayin ma’aunin nisabin Zakka a jihar Kano wanda Kimarsa ta kai naira dubu Dari tara da tamanin da biyar a yau.
2. Zaman ya amince cewa Sadaki yarjejeniya ce tsakanin waliyan yarinya da wakilan Ango wanda za suyi la’akari da wadatar mai Aure da Kimar wacce za’a aura da halin da ake ciki, amma duk yarjejeniyar da za suyi kada sadakin ya Gaza naira dubu asirin.
3. Diyyar Rai ta kama naira miliyan dari da hamsin. Amma ga wanda ya yi kisan ganganci, za’a koma ga mataki mafi tsauri, wanda Alkali zai fitar da shi a wajen yin hukunci.
4. Za’a rika yin wannan zama duk bayan wata uku domin yin duba ga wannan batutuwa.
5. Za’a sanar da gwamnatin wacce zata kirawo taron wayar da kai da na ‘yan Jaridu da kuma isarwa ta hanyar da duk ta dace. Hakazalika suma sauran majalisar Malamai da hukumomin da abin ya shafa zasu taimaka wajen isar da sakon.
Tunda farko, shugaban hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano Barista Habibu Muhammad Dan-Almajiri ya ce daukar matakin ya biyo bayan yadda a lokutan daban-daban Malamai ke bada mabanbantan Bafawoyi game da nisabin zakka da sadaki da biyan Diyyar Rai.
Dan-Almajiri ya yi fatan Malamai a fadin Jihar Kano za su taimaka wajen Dabbaka matsayar da aka cimma.