• Fri. May 1st, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Hatsari, Shaye-Shaye, Yawan Damuwa Ne Kan Gaba A Janyo Larurar Tabin Hankali — Muktar Na-Wali

BySani Magaji Garko

Oct 10, 2025

DAG: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Masu fama da lalurar Tabin hankali suna bukatar kulawa da ta dace domin inganta rayuwarsu, hakan yasa Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 9 ga watan octobar na kowacce shekara a matsayin ranar masu larurar Tabin kwakwalwa ta duniya.

Taken bikin na bana shine “Mayar da hankali akan Tasirin matsin tattalin arziki kan lafiyar kwakwalwa ga matasa a Najeriya” inda taron ya maida hankali wajen dakile hanyoyin da suke haifar da yawaitar masu Tabin kwakwalwa.

Shugaban kungiyar dake Tallafawa masu Lurarar Tabin kwakwalwa ta kasa Ambassada Alhaji Muktar Na-Wali ne ya bayanan hakan a bikin tunawa da masu larurar tabin kwakwalwa ta duniya wanda ake gudanarwa a duk ranar 9 ga Oktoban wacce shekara.

KU KARANTA: CSADI Ta Tallafawa Mata, Yara Sama Da 600 Da Abinci Mai Gina Jiki, Ta Horar Da Su a Kano

Yace akwai hanyoyi da dama da ake kamuwa da larurar tabin kwakwalwa da suka hadar da Afkuwar hadarin mota da yawan damuwa da matsalolin aljanu da kuma shaye shaye wanda zama annoba a tsakanin allumma.

Yace muddin ba a tashi tsaye wajen yakar matsalolin shaye shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ba, wanda shine jigon fadawarsu cikin Aikata munanan ayyuka da suka hadar da sace sacen wayoyi da sauaran munanan dabiu, to za’a cigaba da samun masu tabun kwakwalwa a tsakanin Al’umma.

Ya ce lokaci yayi da kowane mutum zai bada gudun mowar da ta dace, domin yaki da wadannan munanan dabiu da suka addabi alumma jihar kano dama kasa baki daya.

Ya kara da cewa dole ne a kara sanya ido ga masu sayar da magungunan a cikin unguwanni da masu Kemis domin sune suke sayar da magungunan ga masu shaye shayen.

Daga bisani, Ambassada na wali ya yabawa yan jaridu bisa irin gudun mowar da suke basu wajen wayar da kan alumma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *