Kungiyar tallafawa Marayu da masu karamin karfi CSADI ta tallafawa wani Yaro Usaini Muhammad Tukur da Keken Hawa da kuma kayan makaranta a wani mataki na samar masa abin more rayuwa da kuma samun Ilimi na gari.
Shugabar kungiyar Hajiya Zainab Ahmad Suleiman MFR, JP ta ce sun samawa yaron Keken ne don tallafa masu zuwa makaranta cikin sauki kuma akan lokaci da kuma sauran harkokinsa na yau da kullum.
Mrs Suleiman ta ce la’akari da irin jajircewa da kokarin da yaron yake da shi da kuma karancin abun hanu da iyayensa ke da shi, akwai bukatar karfafa masa gwiwa don cimma burinsa.
KU KARANTA: CSADI Ta Yi Gangamin Wayar Da Kan Mata Kusan 200, Da Yaki da Cutar Tamowa, Duba Aikin Polio a Kano
“Idan ka kula iyayensa basu da karfin sama masa wannan keke, ni kuma da Allah ya hore min to Ina ganin hakan nauyi ne a wuyanmu don tallafa masa, Yana son koyar kere-kere da sana’o’in hannu, to irin wadannan yaran muke so a cikin Al’umma,” inji Zainab Suleiman.
Shugabar da CSADI ta bukaci kungiyoyin masu zaman Kansu, da gwamnatin tarayya da jihohi dama kananan hukumomi da su cigaba da samar da tsare-tsaren tallafawa irin wadannan yaran don samun al’umma ta gari.
Da take jawabi a madadin yaron, Mahaifiyar sa Malama Rabi Muhammad ya godewa shugaban kungiyar CSADI bisa yadda ta tallafawa Danta da Keken hawa kasancewarsa mai bukata da musamman da kuma sauran kayan koyo da koyarwa na makaranta.
Da yake yiwa GLOBAL TRACKER bayani, Usaina Tukur ya bayyana cewa burinsa shine ya zama kai kere-keren komfiyuta (software engineer) domin bada gudun mowar cigaba rayuwar al’umma musamman masu bukata ta musamman.
Ya kuma bada tabbacin cigaba da jajircewa a harkokin neman Ilimi.