Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, ta umarci Musulmi a fadin ƙasar nan su fara azumin Watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026.
Cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulumin ta fitar a ranar Talata da daddare ta ce an samu bayanan ganin watan a wurare daban-daban a ƙasar nan.
Matakin na alamta shigar watan Ramadan mai alfarma – wanda musulmi a faɗin duniya ke gudanar da ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci biyar.
Don haka ne fadar ta sanar da Laraba 18 ga watan Fabrairu a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan na 1447AH.