Ana Zargin wani Malamin Islamiyya mai suna “Uncle Kamal” a makarantar Islamiyya dake Inusawa a yankin karamar Hukumar Ungogo dake Jihar Kano da yiwa ‘yan Mata su Hudu (4) ‘Yan Gida Daya Fyade lamarin da ya sa har guda daya yanzu bata iya rike bayan gida wato Kashi.
Ana zargin cewa a lokuta mabambanta, Kamal wanda Malamin Islamiyya ne a makarantar Al-Hadeed Private School a Inusawa cikin karamar hukumar Ungogo ya yiwa ‘yan gida Dayan Hassana da Hussaina da kuma Gambo masu shekaru 7 dukkanin su da kuma kanwarsu mai shekaru 5 Fyade, lamarin da ya sa Iyayen yaran kaddamar da bincike da tallafin kanin mijinta Mai suna Abdulyasar Ayuba Madaki.
“Yaran uku daga cikin wadanda abun ya faru da su ‘yan hudu (4) ne aka haifesu a shekarar 2019, Hassana da Hussaina da Gambo sai kuma na hudun wanda shi Namiji ne kaga yanzu suna da shekaru 7, to Namijin Yana can wajen kakaninsa, sai kuma kanwarsu wacce ita kuma yanzu shekarunta 5 da haihuwa,” inji Madaki.
KU KARANTA: Tsofaffun Leburorin Isiyaka Rabi’u a Rivers Sun Nemi Tallafin Iyalan Marigayin Da Gwamnatin Kano
Bayan fara bincike likitoci suka tabbatar da cewa anyi lalata da dukkan yaran.
Hakazalika, dukkan ‘yaran sun tabbatar da cewa Uncle Kamal ne yake lalata da su a kan wani teburi a ofis din makarantar.
Lamarin kenan da yasa iyayen yaran karkashin jagorancin Abdulyasar Ayuba Madaki da ya kasancewa kanin mahaifun yaran suka Kai Kara ofishin ‘yan Sanda na Zango dake yankin karamar hukumar Ungogo, bayan sun gudanar da bincike suka mika lamarin zuwa sashen binciken manyan lefuka na rundunar ‘yan sandan Jihar Kano.
Bayan dogon bincike da samun ƙwararan hujjoji, an gurfanar da Malamin nasu Uncle Kamal a gaban Kotun Senior Magistrate No. 27, No-man’s-land, Kano a jiya Litinin 18–05–2026.
Kotun ta aike da wanda ake zargin gidan gyaran hali tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 9 ga Watan Yunin (June) 2026.
A Halin da ake ciki dai ‘Iyaye da ‘yan uwan yaran suna kira ga gwamnatin Jihar Kano da kwamishinan shara’a na Jihar Kano da dukkan Kungiyoyin kare hakkin Dan Adam da su tabbatar an yiwa wanda ake zargi hukuncin lefin da ya aikata la’akari da yadda ‘yan uwan wanda ake zargi da Lauyan sa suna neman a bayar da Belin wanda ake zargin.