• Fri. Jul 17th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Har Yanzu Sana’ar Tura Fina-Finai “Downloading” Halattacciya ce — Abba El-Mustapha

BySani Magaji Garko

Jul 16, 2026

Abba El-Mustapha, shugaban hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ya ce hukumar ba ta soke ko haramta sana’ar downloading a faɗin jiha ba, saboda haka har yanzu Sana’ar Halattacciya ce a dukkan kananan hukumomin Jihar 44.

Hakan na zuwa ne bayan wata sanarwa da Mukaddashin Babban Kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar Kano Mujahid Aminundeen ya aikewa ‘yan Jaridu ciki harda wakilin GLOBAL TRACKER cewa an haramta Sana’ar ne saboda wasu na yin amfani ita wajen tura Fina-Finan da ke watsa tarbiyar al’umma musamman mata da matasa.

To sai dai, a cikin wata sanarwa da GLOBAL TRACKER ta gani, shugaban hukumar ta ce Fina-Finan Kano Abba El-Mustapha ya ce har yanzu hukumar bata haramta sana’ar ba.

KU KARANTA: Hisbah Ta Haramta Sana’ar Tura Fina-Finai Ta “Downloading”

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hanun mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, a yau Alhamis, ta ce babu wata hukuma da ta tuntuɓi hukumar tace Fina-finai da dab’i kafin ɗaukar irin wannan mataki, duk da cewa masu sana’ar downloading na daga cikin waɗanda hukumar ke da alhakin sa ido kan ayyukansu bisa tanadin dokar da ta kafa ta.

Haka kuma Hukumar ta ce tuni ta fara bincike kan wani saƙon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin wasu masu sana’ar da yaɗa bidiyoyin tsiraici.

To sai dai ta ce binciken farko ya nuna muryar da ke cikin saƙon ba daga Jihar Kano take ba, yayin da bincike ke ci gaba.

A cewar sanarwar, hukumar ta tura jami’anta a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin gano masu yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya, tare da ɗaukar matakin doka a kansu idan aka same su da aikata laifi.

Hukumar ta kuma ce ta yi la’akari da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin masu sana’ar downloading da masana’antar Kannywood, tare da muhimmancin samar wa matasa hanyoyin samun abin dogaro da kai. Saboda haka, ta jaddada cewa ba ta haramta sana’ar ba, sai dai za ta ci gaba da hukunta duk wanda aka kama yana amfani da ita wajen yaɗa abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *