Wata gobara da har yanzu ake cigaba da binciken asalin tashin ta, ta yi sanadiyar konewar dukkan babban Asibitin garin Tiga (Tiga General Hospital) da ke Karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano.
A kwarya kwaryar binciken da GLOBAL TRACKER ta gudanar ya gano cewa Gobarar ta faro ne a sashin kula da lafiyar mata wato (Maternity), ta kuma tsallaka zuwa sashin tayata na Asibitin da ma sauran sassan Asibitin Baki daya.
Daya daga cikin likitocin Asibitin Dakta Aminu ya shaidawa ‘Yan jaridu cewa Wutar ta tashi sau biyu a Asibitin, kuma sunyi nasarar kashe ta Farko, amma ta biyu ta ci Karfin su.
“Wutar ta tashi ne da misalin karfe 12:00 na safe, kuma ta fara ne daga kasa, wanda akayi kokari aka kashe ta akan lokaci domin ko hayaki babu a cikin Asibitin, lokacin da abin ya faru, bamu san harshen Wutar ya taba ‘ceiling’ ba, to amma daga Baya sai muka sake ganin hayaki ta cikin ceiling ta sama kenan kuma munyi kokarin mu domin kashe Wutar amma abin ya ci tura.”
KU KARANTA: Za Mu Zabi Gawuna Don Zama Gwamnan Kano — Rabi’u Tumfafi
“Muna tunanin Wutar ta cikin ‘ceiling’ ta sake tashi, Kuma munyi iya kokarin mu domin kashe Wutar amma abin ya ci tura domin kusan komai ya Kone a Asibitin, abinda da ta bari Bai taka Kara ya karya ba”.
Dakta Aminu ya kuma shaida mana cewa tuni aka Samar da guri na wucin gadi domin cigaba da kula da lafiyar wadanda aka yiwa tayata da kuma sauran marassa lafiya.
Haka zalika wani shaidar Gani da Ido a garin Abba Tiga ya shaidawa ‘Yan jaridu cewa saboda tsananin zafin Wutar a kwanukan rufun Asibitin ne suka Rika tashi sama.
To amma wasu majiyoyi da basu so a bayyana sunan su ba sun bayyana mana cewa Gobarar ta samo asali ne daga Robar Shinkafa da aka Kona a Asibitin.
Majiyar dai ta tabbatar da cewa a harabar Asibitin aka noma shinkafar kafin daga bisani Robar kuma aka Kone ta wacce tayi sanadiyar tashin Gobarar.
Da muka tuntubi Mai magana da yawun hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano Samira Suleiman ta sai dai mu tuntubi daraktan dake kula da shiyyar Rano na hukumar domin Karin bayani.
A tattaunarwa da muka yi da shi, Daraktan hukumar Bashir Alhassan Kura ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce sashin kula da lafiyar mata (haihuwa) ne da kuma sashin tiyata kadai ne suka Kone.