• Sat. Jul 12th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Infantino Ya Sake Lashe Zaben Shugabancin FIFA

ByGlobal Tracker

Mar 16, 2023

A Alhamis din nan ne aka sake zaben Gianni Infantino a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, inda zai ci gaba da jagorantar ta har nan da shekarar 2027.

A karo na uku ke nan Infantino mai shekaru 52 a duniya da ya gaji Sepp Blatter a shekarar 2016, ke samun nasarar lashe zaben shugabancin hukumar, bayan amincewa da shi da wakilan da ke zaben shugaban hukumar 211 suka yi.

Duk da cewa dokokin hukumar sun fayyace wa’adi 3 na shekaru hur-hudu na shugabantar hukumar, amma Infantino na shirin ci gaba da jagorantar FIFA har zuwa shekarar 2031, domin a cewarsa shekaru ukun farko da ya yi ba sa cikin lissafi.

KU KARANTA: Juventus ta Dakatar da Pogba Saboda Rashin Da’a

A karkashin jagorancinsa, hukumar ta FIFA ta kara yawan kungiyoyin da ke halartar gasar lashe kofin duniya ta maza daga 32 zuwa 48 wanda za a fara amfani da tsarin a gasar ta shekarar 2026, haka nan a karon farko gasar lashe kofin duniya ta mata ita ma aka kara yawan kasashen da ke halartar ta zuwa kungiyoyi 32, kuma a gasar da za a yi a wannan shekarar da kasashen Australia da New Zealand za su karbi bakunci za a fara amfani da tsarin.

 

RFI Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *