• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ana Shirin Binne Dan Wasan Ghana Chiristian Atsu

ByGlobal Tracker

Mar 17, 2023

Ɗaruruwan mutane, ciki har da shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo Ado suka yi bankwana da gawar Christian Atsu, wanda ya mutu a girgizar ƙasa da ta afku a Turkiyya a watan da ya gabata.

Ana gudanar da shirin binne shi ne a Accra, babban birnin ƙasar Ghana.

Cikin mutanen da suka halarci wajen binne ɗan wasan akwai matarsa da kuma ‘ya’yansa da wakilan kungiyar kwallon kafar kasar da kuma na tsohuwar kungiyarsa ta Hatayspor da ke Turkiyya.

READ ALSO: Juventus ta Dakatar da Pogba Saboda Rashin Da’a

An mayar da gawar Atsu zuwa Ghana ne kimanin wata ɗaya da ya gabata bayan gano ta a cikin ɓaraguzai.

Za a binne shi zuwa anjima a yau a mahaifarsa da ke kudu maso gabashin ƙasar Ghana.

Atsu mai shekara 31 ya shafe tsawon rayuwarsa ta kwallon kafa a gasar Firimiyar Ingila, inda ya buga wa kingiyoyi kamar Chelsea da Newcastle da kuma Everton wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *