• Wed. Jun 18th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ku Guji Ta da Hargitsin Siyasa, Mai Unguwar Tukuntawa Ga Al’ummar Kano.

ByGlobal Tracker

Mar 17, 2023

DAGA: ABDULMAJID HABIB ISA TUKUNTAWA, KANO

Tashin hankali baya haifar da da mai ido, sai kawo koma baya ga al’umma da sanadiyar rasa rayukan al’umma wanda hakan bai da ce ba a kowacce al’umma ko gari yankuna ko jihohi harma da kasa baki daya.

Bayanin hakan na cikin jan hankalin da mai unguwar Tukuntawa a karamar Kumbotso dake jihar Kano a arewa maso yammacin Nigeria Alhaji Nuhu Garba Musa Dan-Atumana yayi lokacin da yake jan hankalin al’ummar yankin dangane da muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Dan-Atumana ya kuma yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka kasance tsintsiya da madaurin ki daya a zabukan shugaban kasa da aka gudamar a makonni uku da suka gabata, inda ya bukaci mutane dasu cigaba da zaman lafiya tare kuma da kada kuri’arsu cikin kwanciyar hankali a zaben gwamna da za’ayi a gobe Asabar a fadin tarayyar Nigeria.

KU KARANTA: Muna Rokon Al’umma Su Guji Ta Da Hankali a Lokacin Zabe — Sarkin Kano

Nuhu Dan-Atumana ya kara da cewa yankin ya kasance mai zaman lafiya a koda yaushe, a don haka akwai bukatar mutane su cigaba da daukar matakan da suka dace da nufin samin dauwwamammiyar zaman lafiya a yankin.

Cikin wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER ya ce “An yabawa kokarin jagororin jam’iyun siyasu na unguwar Tukuntawa, kan jarumta da dattaku da suka nuna wajen tabbatar da ganin an gudanar da zabukan da suka gabata cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, a fadin unguwar.”

“Wannan yabon ya fito ne daga mai girma mai unguwar Tukuntawa Alh. Nuhu Garba Musa Dan Atumana, cikin wata takardar nuna yabo da jan hankali, mai dauke da sa hannunsa da ya rabawa dukannin jagororin jam’iyun siyasun dake unguwar, sakamakon jajircewa da kishin unguwa da dattaku da suke nunawa adukkanin lokutan gudanar zabuka a unguwar.”
“Dan Atumana, ya kara da cewa duba da yawan al’umar dake unguwar, samun wannan nasarar ta yin zabe lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ya kara daga darajarr unguwar a ciki da wajen jiha.”
“Daga nan sai ya kara yin kira da jan hankulan jagororin, da suka kara daura damara wajen ci gaba da jan hankulan magoya baya da masoya domin kaucewa aikata duk wani abu da ka iya haddasa fitina a yayin da kuma bayan zaben gwamna da yan majalisar jiha, da za’a gudanar ranar Asabar 18/3/23.”
“A karshe, mai unguwa Alh. Nuhu Garba yayi addu’ar Allah ya sa ayi wadannan zabuka lafiya a gama lafiya.”
Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *