• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Hakar Man Fetir a Nassarawa

ByGlobal Tracker

Mar 28, 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙammadar da aikin haƙar rijiyar man fetir a ƙaramar hukumar Obi a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar Nigeria.

Ƙaddamar da aikin tona rijiyar zai sa kamfanin kula da Albarkatun man fetir na ƙasa NNPC ya fara tono man fetir daga jihar.

A cikin watan Nuwamban bara ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe a yankin arewa maso gabashin Nigeria.

KU KARANTA: ZABE: Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro

Yawancin man da ƙasar ke da shi dai tana haƙoshi ne daga yankin Niger Delta a kudu maso kudancin ƙasar nan.

Najeriya dai ta dogara ne kan man fetir da take fitarwa a matsayin hanayr samun kuɗin shiga, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatocin ƙasar ke yi na faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasar.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *