• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An rantsar da Hamza Yousaf Musulmi na farko da ya zama shugaban Scotland

ByGlobal Tracker

Mar 29, 2023

An rantsar da Humza Yousaf a matsayin shugaban yankin Scotland a wani ƙwarya-ƙwaryar buki a birnin Edinburgh.

Humza, ya zama musulmi na farko da ya riƙe muƙamin.

Majalisar dokokin Scotland ce ta zaɓe shi a matsayin shugaban yankin a wani zaman da ta yi ranar Talata.

Sabon jagoran Jam’iyyar ta SNP ya zama mutum na farko daga kabilar da ba ta da rinjaye da zai jagoranci gwamnati bayan samun yawancin kuri’un da aka kaɗa.

Shugabannin jam’iyyu na ɓangaren adawa guda uku – Conservative da Labour da kuma Libs – su suka kalubalance shi a zaɓen.

KU KARANTA: Zulum Zai Gina Kauyuka 3 Don Tsugunar da ‘Yan Gudun Hijira 20,000

Zai fara kafa mukarraban gwamnatinsa a wannan mako, inda zai fuskanci shugabannin ƴan adawa a karon farko a taron amsa tambayoyi a ranar Alhamis.

Mr Yousaf ya samu nasarar zama jagoran Jam’iyyar SNP a ranar Litinin bayan samun kuri’u 26,032, inda ya doke Kate Forbes wadda ta samu kuri’a 23,890, sai kuma Ash Regan da ta zo na uku a zaɓen.

Mista Yousaf ya kasances sakataren lafiya na yankin Scotland kafin zaɓen.

Duk da yadda yakin neman zaɓe ya zafafa, inda aka ga Ms Forbes na caccakar cancantar Mr Yousaf a wata muhawara a gidan talabijin, dukkan ƴan takarar da suka sha kaye sun taya sabon jagoran murna kan nasarar da ya samu, inda suka bukaci jam’iyyar da ta haɗa kai domin mara masa baya.

Da yake magana da gidan talabijin na ITV bayan nasarar da ya samu, Hamza Yousaf ya kwatanta kansa da mutum mai sa’a, inda ya tabbatar wa jama’a cewa zai yi aiki tukuru wajen kawo wa yankin ci gaba.

KU KARANTA: Cin Zaben Abba Gida-gida Nasarar Mutanen Kano Ce — Dr. Shafi’u Kura

Ya kuma ce zai jagoranci kamfe wajen ganin yankin ya samu ƴancin kai.

Ya ƙara da cewa “al’ummar Scotland na son ƴancin kai a yanzu, kuma za mu kasance waɗanda za su jagoranci tabbatar da ganin hakan ya samu.”

Mr Yousaf ya kuma ce zai tambayi gwamnatin Birtaniya da ta bayar da damar sake gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a nan take a ƙasar.

Fadar Downing Street tuni ta ce ba za ta canza matsayar ta kan adawa da kuri’ar jin ra’ayin ba, inda mai magana da yawun firaministan ƙasar ya ce zai fi mayar da hankali kan batutuwan da suke da muhimmanci ga jama’a kamar rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *