• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Raila Odinga Ya Jagoranci Zanga-zangar Adawa da Gwamnatin Kenya

ByGlobal Tracker

Mar 30, 2023

Maduguna yan adawa a kasar Kenya Raila Odinga ya jagoranci gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a yankin Imara Daima a Nairobi babban birnin ƙasar.

Ayarin motocin Odinga sun bi ta hanyar Mombasa da sanyin safiyar yau Alhamis har zuwa wani wuri da ke kudancin garin Embakasi.

KU KARANTA: AU Ta Gamsu Da Shirin Nigeria Na Gudanar Da Sahihin Zabe — Kenyyata

Sauran mutane da suka mara masa baya sun haɗa da mataimakiyar shugaban ƙasa da suka yi takara tare Martha Karua da Kalonzo Musyoka na jam’iyyar Wiper da kuma sauran jagororin ƴan adawa.

Raila Odinga ya ce an kai lokacin da Kenya za ta kuɓuta daga hannun masu mulkin

Ya ce ba za su daina zanga-zanga ba ko da kuwa gwamnati ta kawo miliyoyin ƴan sanda don dakatar da su.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *