DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Cibiyar tallafawa Marayu ta Dakta Adam Kamaluddeen Nama’aji ta samar da kayayyakin sallah ga marayu maza da mata su 100 da suka fito daga unguwannin Maramara da Alfindiki da kududdufawa domin rage musu radadin halin maraici da suka tsinci kansu a ciki.
Shugaban cibiyar Dakta Adam Kamaluddeen Adam Nama’aji ya bayyana cewa ana samar da kayayyakin ne domin tallafawa Marayun dake yankin kasancewa mahaifansu sun rasu adan haka Suna da hakki akan sauran alumma wajen ganin sun basu gudunmawar da ta dace, domin sanya farin ciki a rayuwarsa.
Shugaban cibiyar ya ce sun fara gudanar da da Rabon kayayyakin tallafin ne kimanin Shekaru uku da suka gabata domin tallafawa marayun dake unguwanni Maramara, Alfindiki da kududdufawa domin ganin sun gudanarda da bukukuwan sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
KU KARANTA: Bashariyya Foundation Ta Yiwa Marayu 55 Kayan Sallah
Kimanin marayu 100 maza da mata ne suka Amfana da tallafin kayan sallah, wanda ya hadarda Atamfofi da Yadudduka wanda cibiyar ta raba musu domin rage musu radadi da kuma ganin ta taimakawa wadanda iyayen su suka rasu.
Ya bayyana cewa tallafawa marayu yana daga cikin ayyukan da Allah yake farin ciki dashi, hakan ne yasa cibiyar take zage damtse wajen ganin ta gudanarda Rabon kayayyakin ga Marayun dake yankin.

Daga cikin Marayun da Suka amfana da tallafin kayayyakin sun hadar da Arifullah isah da zainab Yahya sun bayyan farin cikinsu dangane da yadda aka tallafawa rayuwarsu.
Taron ya gudana a farfajiyar makarantar Kamaluddeen islamiyya dake unguwar marmara a karamar hukumar Birni.
Taron ya samu halarta malam Garba Adam Nama’aji da Alhaji magaji lawam da malam Tijjani Alfindiki wakilin shugaban karamar hukumar birni malam Hafiz S. Muhammad da sauran alumma da dama.