• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Shugabannin Afrika na Shirin Sulhunta Rikicin Sudan

ByGlobal Tracker

Apr 19, 2023

Shugabannin ƙasashen Afirka sun ce za su dauki hanyar zuwa kaar Sudan, domin shiga tsakani don kawo karshen faɗan da ake gwabzawa tsakanin bangarorin da ke yaki da juna, da ya janyo mutuwar sama da farar hula 200.

An yi ta jin karar harbe-harbe duk da yarjejeniyar jingine makamai da aka cimma a jiya Talata.

Wakilin BBC ya ce tun ranar Asabar hau yau din nan, bangarorin biyu ke gwabza fada babu kakkautaba, ba alamun za su saduda bare su bada damar da za a kai agaji ga farar hula da fadan ya rutsa da su.

KU KARANTA: Buhari ya Damuwa Kan Yakin da Ake yi a Sudan

Kungiyar Tarayyar Afirka na fatan za a tsagaita domin shugaban Djibouti Ismail Omar Guelleh, da na Kenya William Ruto da na Sudan ta Kudu Salva Kiir su sauka kasar.

Ana fargaba kasar na gab da fadawa yakin basasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *