• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

KANO: Mun Shirya Tsaf Don Nishadartar da Masu Bude Ido — Shugaban Hukumar Kula da Gandun Daji

ByGlobal Tracker

Apr 20, 2023

Shugaban Hukumar Kula da Gandun Daji ta jihar Kano Lawan Jinjiri Kurmawa ya ce sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin tarbar baki a bukukuwan Karamar Sallah da za’a fara a gobe Juma’a.

Kurmawa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Yan jaridu cikin su harda wakilin GLOBAL TRACKER a Kano dake Arewa maso yammacin Nigeria.

Shugaban ya ce sun kawo sabbin dabbobin jeji wadanda babu su a shekarun baya a gidan kula da namun daji na jihar Kano kama daga Wata sabuwar Nau’in Kura da Dila da sauran tsuntsaye wadanda a baya babu su a gidan.

“Munyi hakan ne domin samar da dabbobin da zasu rika hayayyafa da kuma ganin Mutanen da suke ziyartar wannan gida sun bawa idon su abinci don samun Nishadi,” inji Kurmawa.

Wasu daga cikin kadojin da ke gidan
Zarbe

Ya ce akwai sabbin kayan wasannin yara kamar su Lilo da sauran su dukka domin nishadin kananan Yara da zasu ziyarci gidan a lokutan bukukuwan.

Motar wasan yara

 

Kayan wasa na yara.
Kayan wasan da aka tanadarwa yara.
Kayan wasan yara a gidan zoo dake Kano.

Shugaban ya ce sun samar da ingantaccen tsaro la’akari da irin shirin da suka yi na hadin gwiwa daga dukkanin hukumomin tsaro na jihar Kano kama daga ‘yan Sanda da na “civil defense” da jami’an Hisba da ma sauran jama’an tsaro domin ganin an tabbatar da tsaron Mutanen da zasu ziyarci gidan musamman a bukukuwan sallah Karamar ta shekarar 2023.

Shugaban ya cigaba da cewa dukkan ma’aikatan gidan zasu kasance a Shirin ko ta kwana domin tabbatar da cewa sun wayar da kan jama’a yadda dabbobin suke da kuma yadda suke rayuwa a cikin jeji da kuma a gidan.

A cewar shugaban akwai mutane da aka tanada da zasu rika amfani da amsa-kuwwa wajen fadakar da al’umma ka’idojin gidan kula da gandun daji tare sanar da mutane Idan sun rasa wani abu mallakinsu ko wani abu Mai kama da haka.

Ya Kuma bukaci al’umma musamman Iyaye da Yara da su guji bawa dabbobi abinci domin wani abincin zai iya zama guba ga wasu dabbobin.

Ya Kuma ce sun dauki matakai daban-daban domin ganin ba’a samu wannan dabi’ar ba ta razana yara ko wani abu Mai kama da haka inda ya ce an tanadi bandakuna ga wadanda suke da bukata da kuma sauran korafe-korafen al’umma.

Rakumin Dawa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *