Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama matashin nan Ibrahim Musa mai shekaru 22 bisa zargin sa da kashe mahaifiyar sa a unguwar Rimin Kebe dake yankin karamar hukumar Ungogo.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na twitter wato @KanoPoliceNG, ta ce ta kama matashin ne a karamar hukumar Dawakin tofa da ke nan jihar Kano da misalin karfe 10 na dare ranar laraba 4 ga watan Mayun 2023.
KU KARANTA: Rundunar Yan Sandan Kano Na Neman Wanda ya Kashe Mahaifiyarsa Ruwa a Jallo
Rundunar ta ce wanda ake zagin ya amsa laifin sa na kisan tare da amsa cewa ya na shaye-shaye.
Ta ce zata gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan yan sanda jihar Kano CP Mohammed Usaini Gumel ya kuma yabawa al’umma bisa irin bayanan da suka bayar da ya kai ga kama wanda ake zargin inda ya bada tabbacin cewa zasu tabbatar doka ta yi aikin ta.