• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zaizayar Kasa Tayi Sanadin Mutuwar Mutane 6 a Congo

ByGlobal Tracker

May 9, 2023

Akalla mutane shida (6) ne suka mutu samakakon wata zaizayar kasa a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu kuma mutane sama da dari (100) suka maƙale a wurin mahaƙar ma’adinai da ya rufta kusa da garin Rubaya da ke Arewacin Kivu.

Ambaliya da zaftarewa laƙa ya shafi ƙauyuka biyu da ke kusa da Tafkin Kivu a makon da ya gabata, inda mutane akalla 400 suka mutu.

KU KARANTA: Mutane 176 Sun Mutu Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa a Congo

An kuma samu rahoton ɓacewar wasu da dama.

Wani mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Patrick Muyaya ya kare gwamnatin kan yadda take kula da iftila’in, bayan suka da mutane ke yi cewa hukumomi ba sa ɗaukar matakin gaggawa kan lamarin da kuma amfani da wagegen rami wajen binne mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *