• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zanga-Zanga Ta Barke Sakamakon Cire Tallafin Man Fetir a Angola

ByGlobal Tracker

Jun 18, 2023

‘Yan sanda a kasar Angola sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutanen da suka fito suna zanga-zanga kan karin farashin man fetur a ƙasar.

Dubban mutane sun fantsama kan tittuna a birnin Luanda da sauran manyan birane domin yin Adawa da Karin farashin man Fetir a kasar bayan cire Tallafin.

Angola da ke ta huɗu a arzikin man fetur a Afirka – ta zabtare kuɗin tallafin da take bayarwa a fetur a watan da ya gabata, lamarin da ya ninka farashin a gidajen mai.

KU KARANTA: Janye Tallafin Man Fetir: Ku Kwantar Da hankalin Ku Abubuwa Za Su Daidaita — Mamuda Zangon Kabo

‘Yan adawa da ƙungiyoyin fararan-hula sun ce an yi gaggawa wajen cire tallafin, tare da kira ga ‘yan sanda su daina amfani da ƙarfi kan masu bore.

BBC Hausa ta rawaito cewa a makon da ya gabata mutane biyar aka kashe lokacin da ‘yan sanda suka buɗe wuta kan direbobin tasi da babura da ke zanga-zanga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *