• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Najeriya ta Sake Kwashe ‘yan ƙasar Ta 126 Daga Sudan

ByGlobal Tracker

Jun 25, 2023

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake kwashe ‘yan ƙasar ta 126 daga kasar Sudan sakamakon rikicin da ake yi a ƙasar tsakanin sojoji da runduna ta musammai yaki da Kwantar da tarzoma wato RSF.

Mutanen da jirgin kamfanin Tarco ya ɗebo sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 4:56 na yammacin jiya Asabar.

KU KARANTA: Za’a Kara Kudi Idan Yakin Sudan Ya Kai Lokacin Hajji – NAHCON

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ita ce ta jagoranci ɗebo mutanen tare da haɗin gwiwar ma’aikatun harkokin waje da ta ‘yan Najeriya mazauna ƙetare, da sauransu.

Sai dai har yanzu akwai ɗaruruwan ‘yan Najeriyar da ke roƙon a kwashe su daga Sudan ɗin amma babu tabbas ko gwamnatin ƙasar za ta ci gaba da aikin kwashe su a yanzu.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *