Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Umar Haruna Doguw ya bada tabbacin farfado da Ilimi a jihar ya na Mai cewa duk wani maaikaci da ba zai bada gudun mowa ba ko kuma zai kawo tasgaro zasu tabbatar anyi waje da shi daga Maaikatar.
Doguwa ya bayyana shirin sa na tabbatar da kudurin gwamnatin Jihar domin farfado da darajar Ilimi.
Yayi wannan kalami ne a yayin ganawar sa ta farko da manyan jami’an ma’aikatar tare da mukaddasan shugabannin sassa dake karkashin ma’aikatar a ofishin sa.
Kwamishinan ya ce babban burin sa shine yaga cewa ya taimaka wajen dawo da daraja da martabar Ilimi a jihar Kano wanda ya sami tasgaro mai yawa a shekarun da suka gabata.
Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na Maaikatar Aliyu Yusuf ya aikowa GLOBAL TRACKER ta Kara da cewa makasudin ganawar sa da Ma’aikatan shine domin su san juna, sannan Kuma su yi masa bayani akan yadda ayyukan su suke domin samun makamar tafiyar da nasa aikin.
KU KARANTA: ‘Mariya Bunkure, Kwararriya Mai Kishin Ilimi a Kano’ — Dahiru Adda’u
Kwamishinan ya tabbatar wa da Ma’aikatan cewa shi mutum ne wanda yake son aiki da mutane masu kwazo da rikon amana wajen gudanar da ayyukan su.
Doguwa ya ce a zaman da zai yi na aiki a ma’aikatar bashi da burin ya musgunawa kowa, burin sa kawai yaga kowa Yana aikin sa yadda yakamata.
“Amma ina mai tabbatar muku da cewa duk wanda bazai bani hadin Kai muyi aiki ba to tabbas zan sa ayi waje dashi na sami chanjin sa domin aikin mu yayi kyau mu samu mu kyautata harkar Ilimi a Jihar Kano” in ji kwamishina Haruna Doguwa.
Kwamishinan wanda ya yaba da yadda yagan fasalin Ma’aikatan, ya ce idan suka zama masu Kara jajircewa to babu shakka bukatar sa zata biya wajen gudanar da aikin da’aka dora Masa alhakin aiwatar wa.