• Mon. Jul 14th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ƙasashen Musulmi na taron Gaggawa a Saudiyya Don Daukar mataki kan Kona Al’qur’ani a Sweden

ByGlobal Tracker

Jul 2, 2023

Kungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (OIC) na gudanar da wani taron gaggawa a birnin Jeddah na ƙasar Saudiya domin nazarin matakin bai ɗaya da za a ɗauka kan ƙona Al’qur’ani mai girma da aka yi a ƙasar Sweden a ranar Laraba.

Tattaunawar wadda Saudiyya ta shirya za ta nazarci matakan da suka dace a ɗauka kan abin abin Allah wadai da Sweden ta aikata.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: An Ga Watan Sallah a Saudia

Tuni dai ƙungiyar ta yi Allah wadai kan abin da matashin ɗan asalin ƙasar Iraki da ke gudun hijira a Sweden ya aikata a wajen babban masallacin Stockholm babban birnin ƙasar Sweden ranar Idin Babbar Sallah.

Akasarin ƙasashen musulmi sun gayyaci jakadunsu da ke Sweden domin nuna ɓacin ransu da kuma aike wa da saƙon Allah wadai.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *