• Sat. May 2nd, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Mayar Da Kano Kayataccen Birni a Shekara Daya — Baffa Bichi

ByGlobal Tracker

Jul 7, 2023

DAGA: KAMAL UMAR KURNA, KANO

Gwamnatin jihar Kano ta ce kafin karshen shekarar nan da muke ciki al’ummar jihar da na duniya zasu ga yadda taswirar zata canza ya zuwa kayataccen birni.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan lokacin da wata kungiyar kwararru masu bincike da nazari akan sauyin yanayi da makamashi suka kawo ziyara fadar gwamnatin kano.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin kano ya wakilta Dakta Baffa Bichi ya ce gwamnatin su ta himmatu matuka wajen dawo da darajar masana’antun jihar wadanda suka durkushe ta hanyar Samar da ingantacciyar wutar lantarki domin gudanar da ayyukansu.

KU KARANTA:Muna Tabbatar Da Tsaftar Guraren Da Suke Da Tarihi a Kano — Zago

Tun da farko da yake jawabinsa, Shugaban rukunin kamfanonin Lee a Najeria kuma shugaban hukumar kwashe shara ta jihar nan Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana cewa daga cikin abin takaicin da yake damun su shine yadda kamfanonin ‘yan asalin jihar Kano suke yin kaura ya zuwa wasu jihohin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *